Bukatar ta kunshi kudin da ya kai $516,333,070, wanda ake sa ran za a samo daga bankin Deutsche Bank, domin gudanar da ayyukan gina sassan 1, 1A da 1B na hanyar mai tsawon kusan kilomita 1,000.
An gabatar da bukatar a cikin wasika da Shugaban Ƙasa ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zauren majalisa a ranar Alhamis.
Tinubu ya bayyana cewa aikin wani bangare ne na manyan ayyukan gwamnati karkashin shirin Renewed Hope Agenda, wanda ke nufin inganta hanyoyin sufuri da tattalin arziki a Najeriya.
A cewar shugaban ƙasa, hanyar za ta ratsa jihohi kamar Sokoto, Kebbi, Niger, Kwara, Oyo, Ogun da Lagos, daga Illela zuwa Badagry.
Ya ce aikin zai taimaka wajen:
inganta haɗin kai tsakanin Arewa da Kudu
rage lokacin tafiya
rage kuɗin sufuri da kaya
inganta kasuwanci da samar da abinci
da kuma haɗa wuraren samar da kaya da kasuwanni da tashoshin ruwa
Tinubu ya kuma bayyana cewa tsarin kuɗin aikin ya haɗa da lamuni mai kariya daga Islamic Corporation for the Insurance of Investment and Export Credit, yayin da gwamnatin tarayya za ta samar da ₦265.5bn domin mallakar fili da biyan diyya.
Za a biya bashin cikin shekaru tara, tare da lokacin alfarma na tsawon shekaru uku, kuma ribar zai kasance bisa tsarin SOFR tare da ƙarin kashi 5.3 cikin dari.
Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta riga ta amince da tsarin kuɗin aikin kafin a mika shi ga Majalisar Dattawa.
A zaman majalisar, ‘yan majalisa sun bayyana cewa aikin na da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin ƙasa, musamman wajen rage tazara tsakanin Sokoto da Lagos daga kusan awa 13 zuwa awa 6.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce aikin zai iya zama wani babban abin da zai inganta tattalin arziki da rayuwar ‘yan Najeriya.
Ya tura bukatar zuwa kwamitin majalisa kan bashin cikin gida da waje, tare da umartar su da su kawo rahoto cikin mako guda.
