halin yanzu, Manchester City ce ke kan gaba a teburin gasar bayan ta doke Burnley da ci 1-0 a ranar Laraba da dare.
Sai dai City tana kan gaba ne kawai da bambancin kwallaye, yayin da ita da Arsenal ke da maki ɗaya da kuma kusan daidaiton bambancin kwallaye.
Arsenal na da damar komawa saman teburin idan ta karbi bakuncin Newcastle a wannan karshen mako. Haka kuma za ta buga wasa da Fulham kafin Manchester City ta je wasan Everton a gasar.
Da yake magana a tashar Sky Sports, Merson ya ce: “Daga babu inda ake tsammani, Manchester City ta sake zama a saman teburin gasar. Abin ban tsoro ne.”
Ya kara da cewa: “Amma Arsenal za ta buga wasanni biyu kafin City, kuma za ta iya sake yin tazarar maki shida. Dole ne su yi amfani da wannan dama. Dole ne su ci Newcastle da Fulham domin su matsa wa City lamba. Wannan wasa ne mai matukar muhimmanci.”
