An bayyana wannan umarni ne a cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce wannan mataki ya zo ne domin bin dokokin da ke kunshe a cikin Electoral Act 2026 (as amended).
“Wannan umarni ya yi daidai da dokokin da ke tsara yadda masu rike da mukaman gwamnati za su shiga harkokin zabe,” in ji Gidado. DALILIN UMARNIN
Gwamnatin ta bayyana cewa matakin na da nufin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin zabe, tare da hana rikice-rikicen anfani da mukamin gwamnati wajen neman kuri’u.
UMARNIN MIƘA MULKI
Haka kuma, an umarci duk wadanda abin ya shafa da su mika:
dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu
da kuma ayyukan ofisoshinsu
ga jami’an da suka dace a ma’aikatunsu (MDAs).
GODIYA DAGA GWAMNATI
Gwamnatin jihar Bauchi ta gode wa dukkan wadanda abin ya shafa bisa gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a kokarinsu na neman mukamai a gaba.
