Wani ɗan Amurka mai aikin jinƙai, Alex Barbir, ya musanta zargin cewa kalamansa ko ayyukansa na da alaƙa da tayar da rikici a wasu sassan Najeriya, musamman a jihohin Plateau da Benue.
Barbir ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a tashar TVC News, inda ya ce aikinsa na mayar da hankali ne kan kare rayukan jama’a da taimakawa wajen sake gina al’ummomi da suka fuskanci rikici.
Ya ce bai taɓa kiran kowa da a kashe wani ba, yana mai cewa duk abin da yake kira shi ne a kare rayuka da kuma inganta tsaro.
Dangane da zargin cewa kalamansa na ƙarfafa tashin hankali, Barbir ya ce hakan ba gaskiya ba ne, yana mai cewa rikice-rikicen da ake gani a yankunan sun daɗe suna faruwa tun kafin zuwansa.
Ya kuma ce idan gwamnati ta gaza samar da tsaro, mutane na da damar kare kansu daga barazana, sai dai ya jaddada cewa manufarsa ba tayar da hankali ba ce.
Barbir ya ce yana shirin komawa Najeriya domin ci gaba da ayyukan sake gina gidaje, makarantu da wuraren ibada a jihohin Benue da Plateau, inda ya ce duk ayyukansa na da manufar taimako da zaman lafiya.
Ya bayyana cewa yana samun tallafi daga kungiyoyin agaji da coci-coci, yana mai musanta cewa yana aiki da wata manufar siyasa ko ta waje.
