Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da yawaitar hare-haren tashin hankali da ake fuskanta a sassan Najeriya, yana mai bayyana su a matsayin barazana ga zaman lafiya, hadin kai da kuma dorewar kasar.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter) a ranar Asabar, Atiku ya soki abin da ya kira “ci gaba da ayyukan ta’addanci da fashi da makami,” yana mai jaddada cewa irin wannan tashin hankali da ake yi wa fararen hula bai kamata ya zama abin da zai bayyana al’ummar Najeriya ba.
Ya kuma mika ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu da kuma al’ummomin da lamarin ya shafa, tare da kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen magance matsalar tsaro da ke addabar kasar.
A cewarsa:
“Babban alhakin kowace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Don haka, wajibi ne a dauki matakai cikin gaggawa, da hadin kai da kuma azama domin shawo kan wannan kalubale da dawo da amincewar jama’a.”
Haka zalika, Atiku ya yaba da goyon bayan da gwamnatin Amurka ke bayarwa a yaki da ta’addanci, yana mai jaddada muhimmancin ci gaba da hadin gwiwar kasa da kasa wajen yakar matsalar tsaro.
Wannan furuci na Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar sabbin hare-hare masu muni a wasu sassan kasar.
A jihar Borno, wani hari da aka kai kan sansanin soji da ke Benisheikh ya yi sanadin mutuwar sojoji na rundunar 29 Task Force Brigade karkashin Operation HADIN KAI, ciki har da Brigadier Janar O.O. Braimah. Harin ya kuma jawo lalacewar motoci da gine-ginen sojoji.
