Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar da dakatar da shirin fitar da marasa lafiya daga Gaza bayan kashe wani ma’aikaci da ke aiki tare da su a ranar Litinin.
Shugaban hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana cewa sun shiga cikin alhini sakamakon wannan lamari, inda ya tabbatar da cewa an kashe mutumin ne yayin wani hari da ya shafi tsaro a yankin.
A cewarsa, wasu ma’aikata biyu sun kasance a wurin lokacin da lamarin ya faru, amma ba su samu rauni ba.
Bayan wannan lamari, WHO ta dakatar da fitar da marasa lafiya daga Gaza ta hanyar Rafah zuwa ƙasar Masar, inda ake kai su domin samun kulawa ta musamman.
Hukumar ta ce za a ci gaba da dakatar da wannan aiki har sai an samu tabbacin tsaro a yankin.
Ana sa ran wannan mataki zai iya ƙara jefa marasa lafiya cikin mawuyacin hali, musamman waɗanda ke buƙatar kulawar gaggawa a wajen Gaza.
