Rundunar ‘Yan Sanda ta Kano ta yi nasarar cafke wani fitaccen ɗan daba tare da abokinsa bayan bidiyoyinsu suna girgiza makamai sun mamaye kafafen sada zumunta. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya gargadi cewa duk wanda ya kuskura ya ɗora bidiyo na tashin hankali ko nuna makami a yanar gizo zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Add A Comment