A daidai lokacin da damuna ta yi nisa, hankalin mutane musamman waɗanda suke zauna a yankunan da ake hasashen samun ambaliyar ruwa sun fara shiga damuwa saboda fargabar halin da za su iya shiga.A Najeriya, duk shekara, ambaliyar ruwa daga manyan madatsun ruwa daga cikin ƙasar da ma maƙwabta na haifar da asarar rayuka, lalata amfanin gona da kuma ruguza gidaje a ƙasar.
A shekarar da ta gabata, ambaliya ta ɗaiɗaita birnin Maiduguri, lamarin ya jawo asarar rayuwa da asarar ɗimbin arziki, wanda har yanzu waɗanda abin ya shafa ba su gama warwarewa ba.
Haka kuma a bana an yi ambaliyar ruwa a garin Mokwa da ke jihar Neja, wadda ta jefa mutanen yankin cikin tashin hankali.
Sai dai kamar abin da masu iya magana ke cewa, an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa, haka wasu ke cewa game da ambaliyar ruwa a Najeriya, kasancewa lamarin ya yawan maimaituwa, duk da matakan da gwamnatoci a matakai daban-daban suke cewa suna ɗauka.
A daidai lokacin da damuna ta yi nisa, hankalin mutane musamman waɗanda suke zauna a yankunan da ake hasashen samun ambaliyar ruwa sun fara shiga damuwa saboda fargabar halin da za su iya shiga.