Wani batu da ke jan hankali a siyasar Najeriya shi ne yadda bayanai ke cewa babbar Jam’iyyar adawa ta PDP ta na lallaɓa tsohon shugaban ƙasar GoodLuck Jonathan domin ba shi tikitin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027
Mista Jonathan ya ja baya a harkokin siyasa tun da ya fadi zabe a 2015, kuma jam’iyyar PDP ta tabbatar da cewa tana tattaunawa da shi domin ya yi mata takarar shugaban ƙasa don kalubalanar shugaba Bola Tinubu a zaɓe mai zuwa.
Wasu masana na ganin cewa wannan mataki ne na gurgunta tafiyar haɗakar wasu manyan yan’awar ƙasar.
Majiyoyin sun shaida wa BBC cewa jam’iyyar ta PDP a hukumance, da kuma a matakin wasu jiga jigan ta, ciki har da gwamnoni ne ke wannan yunkuri na zawarto tsohon shugaban Najeriyar Good Luck Ebele Jonathan dominn ba shi takara a jama’iyyar a zaben 2027.
Malam Ibrahim Abdullahi, shine mataimakin sakataren yaɗa labaran jam’iyyar ta PDP, ya kuma tabbatar da wannan yunƙuri yana mai cewa tsohon shugaban Najeriyan ya nuna yiyuwar amincewa da wannan buƙata.I’m