Gwamnatin Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da shan suka kan zargin fifita jihar Lagos a ayyukan raya kasa, musamman daga wasu ‘yan yankin arewacin kasar.
Wannan batun ya janyo ce-ce-ku-ce a baya-bayan nan a kasar tsakanin wasu ‘yan arewacin Najeriyar da kuma masu kare gwamnatin ta Tinubu, kan zargin shugaban ya fi bayar da fifiko wajen samar da manyan ayyukan cigaban kasar, yayin da wasu jihohi da yankuna ke fama da matsalolin tsadar rayuwa da
tabarbarewar ababen more rayuwa.
‘Yan siyasa da masu fafutukar kare hakkin bil’adama daga arewacin kasar na zargin gwamnatin da rashin nuna kulawa ta musanman, kamar yadda gwamnatin ke nuna kulawa da jihar Lagos, maimakon gaba dayan kasar musamman ma arewaci.
Masu sukar na cewa hakan ya ta’azzara matsalar tattalin arziki da kuma zamantakewar al’ummar yankin na arewa.