Babban attajirin Najeriya, Aliko Dangote, ya bayyana cewa nan da shekara guda ko fiye, ba za a ƙara shigo da taki daga ƙasashen waje zuwa Afrika ba.
A cewarsa, masana’antar takin zamani da ya kafa a Legas yanzu haka na samar da tan miliyan 3 na urea duk shekara. Amma sun kammala shiri don ninka wannan yawan, har su wuce ƙasashen da suka fi fitar da taki kamar Qatar.
Dangote ya ce hakan zai taimaka wajen rage dogaro da takin waje, da kuma samar da ayyukan yi ga matasa, da ceto kudin waje (forex) da Najeriya ke asarawa.
> 🔹 “Muna kokarin ceto Afrika daga dogaro da kasashen waje a fannin abinci.” – inji Dangote
🟦 Asrah 24 TV – Gaskiyar Zance
