Close Menu
  • Home
  • News
    • National
    • International
  • Asrah 24 TV
  • Education
  • Health
  • Podcast
  • Politics
  • Sports
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
Facebook X (Twitter) YouTube WhatsApp Telegram
Facebook X (Twitter) WhatsApp Telegram
ASRAH 24 MEDIA
Subscribe
  • Home
  • News
    1. National
    2. International
    3. View All

    Najeriya Ta Kai Dala $18.4 Biliyan a Cinikayyar Cikin Afirka a 2024

    June 28, 2025

    Afreximbank Ta Ba Najeriya Tallafin $50 Biliyan Don Manyan Ayyuka

    June 28, 2025

    Mutane 28 sun mutu sakamakon gudun wuce sa’a a jihar Ondo- FRSC

    February 2, 2025

    Najeriya Ta Fuskanci Limit na Visa zuwa Amurka – 3 Mako Kaɗai!

    July 9, 2025

    Gwamnatin Tarayya Tare da Faransa Za Su Inganta ICT a Jami’o’in Najeriya da Tallafin Naira Biliyan 38

    July 4, 2025

    Zafin Rana Mai Tsanani Ya Ɓarke a Turai: Matsalar Heat Dome

    June 30, 2025

    Najeriya Ta Samu Jarin Waje Har Dala Biliyan 2.5 Daga Masarautar Saudiyya

    June 29, 2025

    Tiwa Savage Ta Bayyana Yadda Take Rashin Kulawar Don Jazzy Da Mavin

    May 20, 2026

    NERC Da ONSA Sun Hada Kai Don Dakile Lalata Kayan Wutar Lantarki

    May 20, 2026

    Iran Ta Shirya Auren Jama’a Ga Masu Shirin Sadaukar Da Rayukansu A Yaki

    May 19, 2026

    NUJ-FCT Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yada Labaran Karya Gabanin Zabuka

    May 19, 2026
  • Asrah 24 TV
  • Education

    Sojojin Najeriya Sun Yaye Sabbin Paratroopers Bayan Kammala Horon Tsalle Daga Jirgin Sama

    June 5, 2026

    Achievers University Ta Bankado Zargin Damfarar Kudin Makaranta Ta N457.5m

    May 25, 2026

    NYSC ta shawarci iyaye su taimaka wa ‘ya’yansu da karin kudin tafiya

    May 21, 2026

    NYSC ta tsawaita wa wasu masu bautar kasa hidima a Gombe

    May 21, 2026

    Najeriya da Italiya sun hada kai domin tara dala biliyan 5 don tallafa wa ilimi

    May 21, 2026
  • Health

    OYO TA KWANTAR WA MAZAUNA HANKALI KAN CUTAR EBOLA, TA SA MA’AIKATAN LAFIYA CIKIN SHIRI

    June 4, 2026

    Likitan Ondo Sun Ƙara Matsin Lamba Kan Gwamnati, Sun Yi Barazanar Tsunduma Yajin Aiki

    May 19, 2026

    Coroner’s Court ta dakatar da shari’ar mutuwar ɗan Chimamanda Adichie har sai umarnin Attorney-General

    May 5, 2026

    Sarki Charles III Ya Yarda Cewa Ciwon Kansar Da Ke Damunsa Na Iya Hana Shi Ganin Dogon Aikin Da Ya Kafa

    April 30, 2026

    Masana lafiya sun bukaci daukar matakin gaggawa kan cutar sickle cell a Najeriya da Afirka

    April 29, 2026
  • Podcast
  • Politics

    Tinubu Torchbearers Zai Taimaka Wajen Wayar Da Kai Da Tallafawa Gwamnati — APC Women Leader

    June 4, 2026

    INEC Ta Shirya Tsaf Domin Zaben Sanatan Ondo Kudu Ranar 20 ga Yuni

    June 4, 2026

    LP Ta Kammala Zaben Fidda Gwani, Ta Tsayar da ‘Yan Takara na Majalisa a Anambra

    June 4, 2026

    Peter Obi Ya Kare Adeboye, Ya Gargadi Matasa Kan Rarrabuwar Kabilanci Da Addini

    June 4, 2026

    Tsohon Firaministan Senegal Ousmane Sonko Ya Zama Kakakin Majalisa

    May 26, 2026
  • Sports

    Shaibu Ya Yabawa Super Eagles Da Adeboye Kan Nasarorin Unity Cup Da Wasan Poland

    June 4, 2026

    Super Eagles Na Da Ƙarfin Doke Kowace Ƙasa Duk Da Rashin Tikitin Gasar Kofin Duniya

    June 4, 2026

    Kai Havertz Ya Yabawa Jamus Karfin ‘Yan Hari Gaban Gasar Kofin Duniya Ta 2026

    June 4, 2026

    Marinakis Ya Yi Rikici A Athens Yayin Gasar EuroLeague

    May 25, 2026

    Spurs Sun Farfado Thunder, Wembanyama Ya Jagoranci Nasara A Wasan NBA

    May 25, 2026
  • More
    • Agriculture
    • Business
    • Climate Changes
    • Culture
    • Environment
    • Entertainment
    • Opinion
    • Religious
    • Security
    • Videos
ASRAH 24 MEDIA
Home » Tarihin Marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata
News

Tarihin Marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata

Asrah24 MediaBy Asrah24 MediaJune 28, 20253 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp
Polish 20250628 122932171

Alhaji Aminu Alhassan Dantata dai ya yi karatunsa na share fage daga 1938 zuwa 1945 a makarantar Firamare ta Dala, kuma ya halarci Makarantar Turanci da Larabci ta Dantata tsakanin 1945 zuwa 1949.

Mahaifinsa, Alhassan Dantata, an haife shi a shekara ta 1877 kuma ya rasu a ranar 17 ga watan Agustan, 1955, ɗan kasuwa ne a fannin kayayyakin amfanin gona, wanda ke tallata hajarsa kasashe daban daban na Duniya.

Marigayi Aminu Dantata ya yi saurin koyi da kasuwancin mahaifinsa kuma ya yi fice sosai a fagen kasuwancin.

Ya fara harkokinsa na kasuwanci a matsayin mai siyen kayayyaki ya siyar a shekarar 1949 a kasuwancin dangin kamfanin Alhassan Dantata and Sons Limited, ya zama Shugaba kuma Manajan Daraktan Kamfanin a 1960.

Ya kasance memba na Kwamitin Gudanarwa na Bankin bunkasa Masana’antu na Najeriya, ya kuma zama Daraktan Bankin tsakanin 1962 zuwa 1966.

Alhaji Aminu Dantata shi ne wanda ya kafa kamfanin Express Petroleum and Gas Company Limited kuma yana daga cikin mutanen da suka jagoranci Bankin Jaiz a kasar nan.

Fitaccen dan kasuwar dai ya jagoranci ayyukan kasuwanci da yawa zuwa ƙasashe daban daban na Duniya.

A wata hira da akai dashi lokacin yana Raye a matsayinsa na wanda ya kafu a harkar kasuwanci, Alhaji Aminu Dantata ya yi imanin cewa kasuwanci yana da maganin rashin zaman lafiya da rashin aikin yi.

A cewar sa sai anyi kasuwanci za a samu masana’antu kuma mutane za su sami kwanciyar hankali a harkokin kasuwancinsu, kuma shugabanni za su mallaki talakawansu kuma su bunkasa al’umma a dukkan matakai.

Alhaji Aminu Dantata baya ga manyan nasarori da ya samu a kasuwanci ya kuma jefa ƙafafun sa a harkar siyasa a cikin kasar nan kasancewarsa ɗan majalisar wakilai na lokaci ɗaya a jihar Kaduna a lokacin Jamhuriya ta Farko, sannan kuma ya kasance mamba a majalisar lardin Kano.

Ya kuma taba rike mukamin mamba na sabuwar Jihar Kano da aka kafa a shekarar 1967, inda ya yi aiki a matsayin kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar a karkashin marigayi Audu Bako, gwamnan Kano a lokacin gwamnatin soja ta Janar Yakubu Gowon.

Gabanin Jamhuriya ta Biyu, wacce ta samar da marigayi Alhaji Shehu Shagari a matsayin shugaban kasa, Alummar kasar nan daga sassa daban daban sunta kiraye-kiraye kan ya fito takarar shugabancin Najeriya sai dai yayi watsi da kiran nasu inda bai fitoba.

Ana dai kallon Marigayi Aminu Dantata a matsayin daya daga cikin mawadata mafi alkhairi a kasar nan, wanda kyautatawarsa ya canza rayuwar mutane da dama.

Alhaji Aminu ne ɗa na ƙarshe wanda ke da rai a cikin ‘ya’yan Alhaji Alhassan Dantata.

Alhaji Aminu Alhassan Dantata dai ya rasu da Asubahin yau a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, yana da shekara 94 a Duniya.

Aminu Dantata, kawu ne ga shahararren mai kuɗin nan na Afirka Alhaji Aliko Dangote.

Share. Facebook Twitter Telegram WhatsApp
Previous ArticleGanduje ya aje shugabancin Jam’iyyar APC na Kasa
Next Article Afreximbank Ta Ba Najeriya Tallafin $50 Biliyan Don Manyan Ayyuka

Related Posts

Tiwa Savage Ta Bayyana Yadda Take Rashin Kulawar Don Jazzy Da Mavin

May 20, 2026

NERC Da ONSA Sun Hada Kai Don Dakile Lalata Kayan Wutar Lantarki

May 20, 2026

Iran Ta Shirya Auren Jama’a Ga Masu Shirin Sadaukar Da Rayukansu A Yaki

May 19, 2026

NUJ-FCT Ta Gargadi ‘Yan Jarida Kan Yada Labaran Karya Gabanin Zabuka

May 19, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

Latest Posts

Mummunar Hanyar Kauye Na Hana Yara Zuwa Makaranta A Akwa Ibom — Mazauna Yanki

June 5, 2026

Sojojin Najeriya Sun Yaye Sabbin Paratroopers Bayan Kammala Horon Tsalle Daga Jirgin Sama

June 5, 2026

Dayo Amusa Ta Soki Matsin Lambar Da Ake Yi Wa Fitattun Jarumai Kan Matsalolin Kasa

June 5, 2026

Kungiya Ta Bukaci Hadin Kan ‘Yan Najeriya Wajen Yaki Da Matsalar Tsaro

June 5, 2026

TCN Ta Sanar da Katse Wutar Lantarki a Sassan Delta Saboda Ayyukan Gyaran Tashar Wuta

June 5, 2026
Connect with us
  • Facebook
  • Twitter
  • YouTube
  • WhatsApp
  • Instagram
  • TikTok
Top Posts
Advertisement
© 2026 ASRAH 24 MEDIA. Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.