Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma shugaban riko na jam’iyyar APC Dr. Adbullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam’iyyar na kasa.
Jaridar Primiumtimes ta rawaito cewa ganduje ya bayyana aje shugabancin ne sakamkon rashin Lafiya da take damunsa, inda yanzu zai mayar da hankali wajen neman Lafiya.
Dama dai ana cece kuce kan shugaban na sa sakamakon cikar da Tenure din sa tai.
Sai dai tun daga lokacin da aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na yankin Arewa maso gabas a jihar Gombe, Ganduje ya kara samun matsin lamba sakamakon kin ambatar sunan mataimakin shugaban kasa Kashim Shatima a matsayin wanda zaiwa Tinubu mataimaki a zaben shekarar 2027.
