Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Matasa yan kasa da shekaru 20 Flying Eagles sun doke kasar Egyp a bugun daga kai sai mai tsaran raga da ci 4-1 a gasar cin Kofim Afrika da ake bugawa yanzu haka a kasar ta Egpt.
An fafata wasanne a ranar Lahadi 18 ga watan Mayun shekarar 2025.
Kafin yin bugun daga kai sai mai tsaran ragar dai an tashi a wasan Flyingg Eagles na dai ci 1 yayin da Egypt itama ke da ci 1.
Wannan nasarar ce ta sanya Najeriya ta lashe kyauyar Tagulla karo na biyar kenan a tarihin ta na gasar.
Za dai a fafata wasan neman gurbin na uku a ranar 30 ga watan Yuni mai kamawa a filin wasa na Cairo dake kasar.
Kasar Egypt dai ta shiga gaban Najeriya mintuna 3 da fara wasan ta hannun dan wasa Osama Omar bayan da ya karbe kwallon daga hannun Mahmoud Labib .
Flying Eagles dai ta warware kwallonta mintuna biyu bayan dawowa daga hutum rabin lokaci inda dan wasa Bidemi Amole a mintuna na 47.
