’Yan bindigar da aka yi yarjejeniyar zaman lafiya da su a jihohin Kaduna, Katsina da Neja sun nemi gafara daga al’umma bisa karya yarjejeniyar da suka yi a baya tare da ci gaba da kai hare-hare.
A jiya Laraba, yayin wata tattaunawa da aka sake yi da su a yankunan da aka kulla sulhu, maharan sun bayyana dalilan da suka sa suka karya alkawarin da suka dauka. Sun kuma bada damar bude kasuwannin da suka tilasta a rufe, tare da tabbatar da cewa ba za su sake kai hare-hare ba.
Daya daga cikin shugabannin yankin Birnin Gwari, Kaduna, Zubairu Abdul’rauf, ya tabbatar da samun fahimta da maharan.
Yankunan da aka gudanar da zaman sulhun sun hada da Birnin Gwari (Kaduna), Dugun Mu’azu (Sabuwa, Katsina), da wasu yankuna a Jihar Neja.
