Iyalan tsohon shugaban kasa na mulkin soji, marigayi Sani Abacha, sun fara kare martabar mahaifinsu bayan kalaman tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), inda ya zargi Abacha da kitsa hanyoyin kifar da gwamnatinsa ta hanyar tarzoma.
Daya daga cikin ‘ya’yan Abacha, Sadiq S. Abacha, ya bayyana cewa mahaifinsu ya taka muhimmiyar rawa a mulkin Najeriya, kuma har yanzu ana amfana da ayyukansa.
A ranar Alhamis da ta gabata ne aka kaddamar da littafin tarihin rayuwar Babangida, inda a nan ne ya yi wannan bayani. Sai dai Sadiq ya mayar da martani a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa tarihi ba zai manta da gudunmuwar da Abacha ya bayar ba.
