Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya kaddamar da rabon tallafin awakai 3,610 ga mata daga daukacin kananun hukumomin jihar. A jiya Litinin, an fara rabon ne a garin Dan-Nakolo, karamar hukumar Daura, inda kowacce mazaba zata amfana da mata 10.
Gwamnan ya bayyana cewa shirin na da nufin koyar da mata kiwon dabbobi tare da inganta tattalin arzikin su, kuma yana daga cikin burin gwamnati na habaka kiwo a jihar da ma Najeriya baki daya.
An samar da shirin ne da kudin naira biliyan 5.7, wanda zai tallafa wa manoma, musamman kungiyoyin mata. Kowacce mace za ta samu awaki 4 daga mazabun jihar 361.
