Tun bayan tafiyar mataimakin gwamnan jihar Taraba, Aminu Abdullahi Alkali, don neman magani a watan Nuwamba 2024, babu cikakken bayani daga gwamnatin jihar kan halin da yake ciki ko inda yake jinya. Wannan rashin bayani ya haifar da damuwa da cece-kuce a tsakanin al’umma da ’yan siyasa a jihar.
A lokacin da aka fara samun labarin rashin lafiyarsa, an ce an kwantar da shi a asibitin tarayya da ke Abuja, kafin daga bisani wasu rahotanni su nuna cewa an mayar da shi kasar Masar sakamakon tsananin rashin lafiyar. Duk da haka, babu wata sanarwa ta hukuma da ta tabbatar da wadannan bayanai.
Al’ummar jihar Taraba na ci gaba da kira ga gwamna Agbu Kefas da ya bayyana gaskiyar halin da mataimakinsa ke ciki, domin kawar da jita-jita da kuma tabbatar da cewa jama’a sun samu sahihin bayani kan lamarin.
Kokarin jin ta bakin kakakin majalisar dokokin jihar, John Kizito, ya ci tura, kasancewar yana wata tafiya zuwa kasashen ketare. Haka zalika, gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan batun rashin lafiyar mataimakin gwamnan ba, lamarin da ke kara haifar da rashin tabbas a zukatan jama’a.
