Kungiyar Transparency International ta fitar da sabon rahoto kan cin hanci da rashawa a duniya, inda Najeriya ta samu matsayi na 140 daga cikin kasashe 180 a shekarar 2024. Rahoton ya nuna cewa Najeriya, tare da Mexico, Madagascar, Uganda, Iraqi, da Kamaru, sun samu maki 26 daga cikin 100 a ma’aunin da aka yi amfani da shi. A cewar kungiyar, kasar Denmark ce ta fi fuskantar cin hanci a bana, yayin da Somaliya, Venezuela, da Sudan ta Kudu suka kasance kasashen da suka fi fama da cin hanci da rashawa.
