Gwamnatin Najeriya ta dauki matakan hana shigowar cutar Ebola cikin kasar, yayin da Hukumar Dakile Yaduwar Cutuka (NCDC) ta kara kaimi wajen binciken matafiya a filayen jiragen sama don gano masu dauke da cutar.
Shugaban NCDC, Dr. Idris Jide, ya bayyana cewa kawo yanzu ba a samu wani mutum da ya shigo Najeriya da cutar ba. Sai dai gwamnati ta gargadi ‘yan kasa da su takaita tafiye-tafiye zuwa kasashen da cutar ta bulla.
A baya-bayan nan, hukumomin Uganda sun tabbatar da barkewar cutar a yankunan Mbale, Mukono, da Wasiko tun a karshen watan Janairu, inda aka rasa rai daya tare da zargin kamuwar mutane 44.
