Rahotanni sun bayyana cewa mutane biyu sun rasa ransu, yayin da hudu suka jikkata sakamakon rikicin da ya barke a lokacin rusau a unguwar Rimin Zakara, Kano.
Mazauna yankin sun ce jami’an tsaro ne suka harbe mutanen da suka mutu yayin da ake aiwatar da rusau din karkashin jagorancin wakilan gwamnatin jihar.
A cewar wasu shaidu, an rushe gidaje fiye da 50 a daren jiya Lahadi, wanda ya haifar da asarar dukiya mai yawa tare da barin mutane da dama cikin mawuyacin hali. Wasu fusatattun matasa sun zargi jami’an da yin rusau ba tare da bin umarnin kotu ba, lamarin da ya janyo hargitsi har aka yi harbin da ya yi sanadin mutuwa da raunuka.
Kawo yanzu, gwamnatin Kano ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
