Jami’ar Bayero dake jihar Kano ta samar da cibiya ta musamman da za ta rinka gudanar da bincike kan irin illar da miyagun kwayoyi ke sanya dan adam aikatawa.
Shugaban sashin Fasahar sarrafa kwayar halittar dan Adam wato Biotechnology a Jami’ar Farfesa Anas Ibrahim Yahaya Bichi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Freedom Radio.
Ya kuma ce suna da injina na musamman da za a iya yin bincike da su kan abubuwan da suka shafi muhalli da ayyukan Noma.
Da yake jawabi mataimkain shugaban cibiyar Dakta Bashir Isah Waziri cewa ya yi, suna da fasahar da za a iya sarrafa shara ta zama Mai da samar da ruwan Sola.
Cibiyar ta Biotechnology dai ta bukaci gwamnatoci a matai daban daban da su hada kai da su wajen magance matsalolin tu’ammali da kwayoyi da kuma inganta tattalin arziki.
