Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da mayar da mataimakan siyasa 28 bakin aiki tare da naɗa sabbin jami’ai takwas, a wani mataki na ƙarfafa gudanar da mulki da inganta ayyukan gwamnati.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse.
Sanarwar ta bayyana cewa waɗanda aka mayar bakin aiki sun haɗa da Mashawarta na Musamman (Special Advisers) 14, Manyan Mataimaka na Musamman (Senior Special Assistants) shida, da kuma Mataimaka na Musamman (Special Assistants) takwas.
Daga cikin mashawartan da aka dawo da su akwai Dr. Atiku Hafiz (Lafiyar Jama’a), Saleh Ahmed Birniwa (Tattara Matasa), Abdurrahman Alkassim (Harkokin Kananan Hukumomi), da sauran su.
Hakazalika, gwamnan ya amince da naɗa sabbin jami’ai takwas bisa cancanta, ƙwarewa da nagarta.
Sabbin naɗin sun haɗa da Farfesa Muftahu Sa’adu Majia a matsayin Mashawarci kan Ilimi Mai Zurfi, Hajiya Salma Wakili kan Harkokin Kasuwanci, Adamu Yusuf Garkuwa kan Harkokin Hajji, Mubarak Aliyu kan Hulɗa Tsakanin Gwamnatoci, da wasu jami’ai.
Sakataren Gwamnatin Jihar ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ƙwarewa da mutunci, yana mai nuna kwarin gwiwar cewa za su taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati da hidima ga al’ummar Jigawa.
Ya ƙara da cewa dukkan naɗe-naɗen da mayar da jami’an bakin aiki sun fara aiki nan take.
