Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana cewa yaƙin da ƙasar ke yi da Iran ya zuwa yanzu ya laƙume kusan dala biliyan 37.5.
Hegseth ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi a gaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattawan Amurka, inda ya nemi amincewa da ƙarin kasafin kuɗi na kusan dala biliyan 67 domin ayyukan Ma’aikatar Tsaro (Pentagon).
Ya ce sabon ƙiyasin ya nuna ƙarin kuɗaɗen da aka kashe idan aka kwatanta da rahoton tsakiyar watan Mayu, wanda ya nuna cewa an kashe kusan dala biliyan 29.
Sakataren ya jaddada cewa ƙarin kasafin kuɗin zai taimaka wajen ci gaba da ayyukan tsaro da kuma biyan buƙatun rundunar sojin Amurka yayin da rikicin ke ci gaba.
