Majalisar dokokin Faransa ta amince da wata muhimmiyar doka da ta haramta wa yara masu ƙasa da shekara 15 amfani da kafafen sada zumunta, lamarin da ya sa Faransa ta zama ƙasa ta farko a Tarayyar Turai da ta kafa irin wannan doka.
Dokar na jiran rattaba hannun Shugaba Emmanuel Macron kafin ta fara aiki, kuma ana sa ran za a aiwatar da ita daga farkon sabon zangon karatu a watan Satumba.
Macron ya bayyana cewa manufar dokar ita ce kare yara daga illolin kafafen sada zumunta da kuma hana kamfanonin fasaha amfani da tunani da motsin zuciyar yara domin kasuwanci.
Ya ce, “Kwakwalwar yaranmu da matasanmu ba kayan sayarwa ba ne, kuma bai kamata a riƙa amfani da motsin zuciyarsu domin riba ba.”
Dokar ta tanadi hana tallace-tallacen da ke ƙarfafa yara su yi amfani da kafafen sada zumunta, ciki har da tallace-tallacen masu tasiri (influencers). Haka kuma, duk wani tallan irin waɗannan kafafe dole ne ya ɗauki gargadin cewa:
“Amfani da kafafen sada zumunta na da haɗari ga yara masu ƙasa da shekara 15.”
Gwamnatin Faransa ta ce za ta samar da tsarin tantance shekaru domin tabbatar da bin dokar, yayin da hukumar Arcom za ta kula da aiwatar da ita.
Rahotanni sun nuna cewa yara masu shekaru tsakanin 12 zuwa 17 a Faransa na shafe kusan awa 1 da mintuna 21 a kullum suna amfani da TikTok, abin da ya janyo damuwa kan tasirin abubuwan da suke kallo ga lafiyar tunaninsu.
Sai dai kamfanonin kafafen sada zumunta sun ce sun riga sun tanadi matakan kare yara daga abubuwan da ka iya cutar da su.