Tsofaffin ‘yan wasan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta cika alkawuran da ta yi wa ‘yan wasan, suna gargadin cewa jinkirin na iya shafar ƙoƙarin ƙungiyar na lashe kofin WAFCON 2026 a Morocco.
Ƙungiyar United Ex-Super Falcons Worldwide, yayin wani taro da ta gudanar a birnin Chicago na Amurka, ta bayyana damuwarta kan yadda har yanzu gwamnati ba ta cika alƙawarin ba wa kowace ‘yar wasa dala 100,000, filin gini da sauran kyaututtuka ba.
Tsohuwar ‘yar wasan Super Falcons, Patience Avre, ta ce rashin cika alkawarin ya rage wa ‘yan wasan ƙwarin gwiwa yayin da suke shirin tunkarar gasar.
Ta ce ‘yan wasan ba sa bayyana damuwarsu a fili saboda tsoron kada a cire su daga ƙungiyar, amma korafe-korafen na ƙaruwa a tsakaninsu.
Avre ta ƙara da cewa rashin ƙarfafa gwiwar ‘yan wasan mata ya daɗe yana hana Najeriya kai matsayin da ya dace a ƙwallon ƙafar mata, duk da irin nasarorin da ƙasar ke samu.
Ta kuma yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, da su tabbatar an cika alkawuran da aka yi wa tsofaffi da na yanzu domin nuna godiya ga gudummawar da suka bayar wajen ɗaukaka sunan Najeriya.
A cewar Hukumar Wasanni ta Ƙasa (NSC), jinkirin bayar da kuɗaɗe, takardun filaye da lambobin yabo ya samo asali ne sakamakon sauya jadawalin sansanin horon Super Falcons kafin gasar WAFCON ta 2026. Duk da haka, tsofaffin ‘yan wasan sun bukaci gwamnati ta gaggauta ɗaukar mataki domin ƙarfafa wa ƙungiyar gwiwa kafin fara gasar.
