Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Benue ta tabbatar da mutuwar mutane takwas bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari a al’ummar Otukpo-Nobi da ke Ƙaramar Hukumar Otukpo a safiyar Lahadi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Udeme Edet, ya fitar, ya ce maharan sun mamaye al’ummar ne da misalin ƙarfe 6:00 na safe, inda suka riƙa harbe-harbe kan mazauna yankin ba tare da bambanci ba.
Rundunar ta ce mutane biyar sun samu raunuka daban-daban a harin, yayin da aka ƙone wasu gidajen ciyawa da kuma babur.
Sai dai alkaluman da ‘yan sanda suka fitar sun bambanta da rahotannin wasu mazauna yankin, inda wasu suka ce mutum 10 ne suka mutu, yayin da wasu kuma suka yi ikirarin cewa adadin ya kai 16.
A cewar rundunar, an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke Otukpo domin kula da lafiyarsu, yayin da aka kai gawarwakin waɗanda suka rasu ɗakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya da ke Otukpo.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Benue, Cletus Nwadiogbu, ya jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya, fara bincike da kuma hana sake aukuwar irin wannan hari.
Rundunar ta kuma ƙara yawan jami’an tsaro a yankin bayan wasu matasa sun gudanar da zanga-zanga sakamakon harin.
‘Yan sandan sun yi Allah wadai da harin tare da miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu da al’ummar Jihar Benue baki ɗaya, sannan suka buƙaci jama’a su bai wa jami’an tsaro cikakkun bayanai da za su taimaka wajen binciken da ake gudanarwa.
