Uchechi Okwu-Kanu, matar jagoran ƙungiyar IPOB da ke tsare, Nnamdi Kanu, ta musanta rahotannin da ke yawo cewa ta shigar da ƙarar neman saki daga mijinta, tana mai bayyana labarin a matsayin ƙarya kuma marar tushe.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X da aka tabbatar da sahihancinsa, Uchechi ta ce ba ta taɓa neman saki ba, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton saboda ba gaskiya ba ne.
Ta nuna damuwarta kan yadda ake ƙirƙirar labarai marasa tushe game da iyalinta ba tare da tantance sahihancinsu ba, tana mai cewa hakan na tauye martabar aikin jarida.
Uchechi ta kuma bukaci jama’a su riƙa amincewa ne kawai da bayanan da suka fito daga gare ta ko wakilanta da ta amince da su. Ta gode wa waɗanda suka tuntube ta domin tabbatar da gaskiyar labarin kafin su yaɗa shi.
Nnamdi Kanu, wanda ya auri Uchechi a shekarar 2009, na ci gaba da zaman gidan yari bayan da wata Kotun Tarayya da ke Abuja ta same shi da laifukan da suka shafi ta’addanci tare da yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Sai dai ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara yana neman a soke hukuncin da aka yanke masa.
