Abuja – Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Cif Eze Chukwuemeka Eze, ya soki Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, kan martanin da ya mayar game da bukatar da ‘yan adawa suka yi na a yi bayani kan zargin da ya shafi FIPC.
Eze ya ce kalaman Wike na yin watsi da bukatar bayyana gaskiya ba su dace da tsarin dimokuradiyya ba, yana mai jaddada cewa jami’an gwamnati suna da alhakin yin bayani ga ‘yan Najeriya kan duk wata shakka da ta taso.
Ya bayyana cewa ba sai mutum yana rike da mukamin gwamnati ba kafin ya nemi a yi gaskiya da rikon amana, yana mai cewa ‘yan adawa suna da hakkin da kundin tsarin mulki ya ba su na sa ido kan ayyukan gwamnati.
Eze ya yi zargin cewa batutuwan da suka shafi FIPC na bukatar cikakken bayani maimakon musayar zafafan kalaman siyasa. Ya kuma yi kira ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ta kasance mai karɓar suka tare da mayar da hankali wajen warware matsalolin da ke damun al’umma.
Hakazalika, ya bukaci Minista Nyesom Wike ya fi mayar da hankali kan inganta ababen more rayuwa, tsaro da ayyukan jama’a a Babban Birnin Tarayya.
Eze ya kuma soki nadin Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban kwamitin kafa ‘yan sandan jihohi, yana mai cewa lokacin bai dace ba saboda zarge-zargen da ake yi dangane da batun FIPC.
A ƙarshe, ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da neman gwamnati ta yi bayani kan ayyukanta, yana mai tabbatar da cewa ‘yan adawa za su ci gaba da sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora musu ba tare da tsorata ba.
