Katafariyar kamfanin kera motoci na Ford ta sake ɗaukar sama da tsofaffin ƙwararrun ma’aikata 300 da suka haɗa da masu duba ingancin motoci da injiniyoyi, bayan tsarin binciken ingancin motoci da ke amfani da Artificial Intelligence (AI) ya kasa cimma sakamakon da ake tsammani.
Rahotanni sun bayyana cewa kamfanin ya fara amfani da AI a wasu sassan ayyukansa domin rage kuɗaɗe da kuma ƙara inganci, ciki har da tantance ingancin motocin da yake kerawa.
Sai dai Mataimakin Shugaban Sashen Injiniyoyin Motoci na Ford, Charles Poon, ya ce kamfanin ya fahimci cewa AI ba za ta iya maye gurbin gogewa da ƙwarewar tsofaffin ma’aikata ba.
Ya ce, “AI kayan aiki ne mai amfani, amma ingancinsa ya dogara da irin bayanan da aka yi amfani da su wajen horas da shi.”
Poon ya amince cewa a baya kamfanin bai ba da isasshen muhimmanci ga ƙwarewar tsofaffin injiniyoyinsa ba, lamarin da ya sa tsarin AI bai yi aiki yadda ake fata ba.
Rahoton Bloomberg ya bayyana cewa kamfanin ya dawo da waɗannan ƙwararru domin su taimaka wajen horas da tsarin AI, na’urar koyon aiki (Machine Learning) da sauran fasahohin zamani, tare da ba matasan ma’aikata horo.
Tun da farko, Shugaban Kamfanin Ford, Jim Farley, ya taɓa bayyana cewa AI za ta sauya yanayin ayyukan ofis da dama, yayin da babban jami’in gudanarwa Kumar Galhotra ya ce kamfanin ya girke kyamarori masu amfani da AI guda 900 a masana’antunsa domin gano matsalolin ingancin motoci tun daga matakin ƙera su.
Sai dai yanzu Ford ta amince cewa wannan fasaha kaɗai ba ta wadatar ba wajen tabbatar da ingancin kayayyaki.
Kamfanin ya bayyana cewa haɗa gogewar tsofaffin ƙwararru da sabbin fasahohin AI ne ya taimaka masa wajen komawa matsayi na farko a binciken JD Power Initial Quality Study, wanda ke tantance ingancin motoci a Amurka.
Ford ta ce wannan ne karo na farko tun shekarar 2010 da ta zama kamfanin kera motoci mafi inganci a rukunin manyan kamfanonin motoci na Amurka.
A cikin sanarwar da ta fitar, kamfanin ya ce wannan nasara ta samu ne bayan sake fasalin shugabanci, ɗaukar sabbin ƙwararru da kuma dawo da tsofaffin injiniyoyi kusan 300 masu ɗauke da gogewar shekaru masu yawa a fannin ƙera motoci.
