Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen Jihar Gombe ta bayyana cewa zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar bai cika ƙa’idojin dimokuraɗiyya ba, tana mai zargin cewa an gudanar da shi ba tare da gaskiya da adalci ba.
Jam’iyyar, wadda ta kaurace wa zaɓen, ta kuma soki gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya kan rushe gine-gine a wasu sassan jihar da kuma korar kamfanin sufuri na Gombawa Motors daga Ibrahim Hassan Dankwambo Mega Motor Park.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na jam’iyyar, Abdulkadir-Ahmad Dukku, ya fitar ranar Talata.
PDP ta bayyana zaɓen da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Gombe (GOSIEC) ta gudanar a matsayin abin kunya ga dimokuraɗiyya, tana mai cewa bai bai wa jam’iyyun adawa damar yin gogayya cikin adalci ba.
Jam’iyyar ta ce dalilin kauracewarta zaɓen shi ne saboda abin da ta kira kura-kurai da rashin bin ƙa’idoji, inda ta yi zargin cewa ba a kai akwatunan zaɓe zuwa rumfunan kaɗa ƙuri’a ba.
PDP ta kuma yi zargin cewa zaɓen ya yi kama da na shekarar 2024, wanda ta ce ya kasance cike da rashin gaskiya.
Baya ga batun zaɓe, jam’iyyar ta zargi gwamnatin jihar da take hakkin al’umma ta hanyar rushe gine-gine, tana mai cewa hakan ya haifar da rashin jituwa tsakanin gwamnati da mutanen da abin ya shafa.
Har ila yau, ta soki wasu kalamai da aka ce gwamnan ya yi a wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta, tana mai cewa irin waɗannan kalamai sun saɓa wa mutuncin ɗan Adam da kuma ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
PDP ta kuma yi Allah-wadai da korar Gombawa Motors daga tashar mota ta Dankwambo Mega Motor Park, tana mai zargin cewa matakin yana da nasaba da siyasa.
Jam’iyyar ta ce ma’aikatan kamfanin suna da cikakken ’yancin bayyana ra’ayinsu na siyasa kamar sauran ’yan ƙasa, don haka bai kamata a hana su gudanar da kasuwancinsu ba.
A ƙarshe, PDP ta buƙaci gwamnatin Jihar Gombe da ta mutunta kundin tsarin mulkin ƙasa, ta kare haƙƙin jama’a, tare da tabbatar da adalci da gaskiya wajen gudanar da mulki.
