Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ya bayyana cewa an yi yankan hadaya ga dukkan mahajjatan da suka biya kuɗin hadaya ta hannun hukumar.
Ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, bayan da wasu mahajjata suka koka cewa sun biya kuɗin hadaya amma ba su ga wata hujja da ke nuna an yi musu yankan rago ba.
Wata sanarwa da Kakakin Gwamna Uba Sani, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata, ta bayyana cewa hadaya ita ce kuɗin da mahajjata ke biya domin a yanka musu dabbobi a ranar 10 ga watan Zul Hijjah.
Sanarwar ta ce wasu mahajjata sun kai ƙorafi ga Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), suna zargin cewa ba a aiwatar da hadayar ba duk da sun biya kuɗi.
Malam Salihu ya ce an wallafa sunayen dukkan waɗanda suka biya hadaya a masaukin mahajjata domin su duba, yana mai ƙalubalantar duk wanda ke da hujjar biyan kuɗi amma sunansa bai bayyana ba ya gabatar da kansa domin bincike.
Ya bayyana cewa mahajjata 827 ne suka biya hadaya a Najeriya kafin tafiya Saudiyya, yayin da 47 suka biya ta hannun NAHCON, sannan 54 suka biya a Saudiyya, wanda ya kai jimillar mahajjata 928 da kuɗin da ya kai Riyal 668,160.
Ya kuma ce an gano cewa wasu daga cikin matsalolin sun fito ne daga mahajjatan da suka biya ta hanyar POS, inda ba a haɗa bayanansu da sunayensu yadda ya kamata ba, amma an gyara matsalar.
Malam Salihu ya tabbatar da cewa kwamitin da yake jagoranta yana aiki cikin gaskiya da amana ga Gwamna Uba Sani, tare da tabbatar da cewa ba za a tauye haƙƙin kowa ba.
