Wani likita da aka yanke wa hukunci a shari’ar mutuwar jarumin Hollywood, Matthew Perry, ya dauki matakin daukaka kara kan hukuncin da aka yanke masa na ɗaurin shekaru 2 da rabi a gidan yari.
Dr Salvador Plasencia ya shigar da ƙara zuwa Kotun Daukaka Kara ta Amurka (Ninth Circuit), inda yake neman a soke hukuncin ko a sake masa zaman shari’ar yanke hukunci.
A cikin takardun kotu, Plasencia ya ce alkali ya yi kuskure wajen ƙara masa hukunci ta hanyar ɗaukar shi a matsayin likita da ya karya amana ta aikin sa.
Lauyoyinsa sun bayyana cewa marigayi Matthew Perry bai nemi magani na gaskiya daga gare shi ba, sai dai ya nemi hanyar samun ketamine domin amfani na kansa. Saboda haka suka ce ya kamata a ɗauke shi a matsayin dillalin miyagun ƙwayoyi, ba likita mai karya amana ba.
Koken kuma ya ce an yi masa hukunci mai tsauri fiye da sauran wadanda ake tuhuma, ciki har da Mark Chavez da Erik Fleming, duk da cewa suna da hannu a irin wannan lamarin.
Dr Plasencia ya amsa laifuka huɗu na rarraba ketamine bayan binciken gwamnatin Amurka ya tabbatar da cewa ya ba Perry maganin a makonnin da suka kai ga mutuwarsa.
Sai dai ya ce ba ya musanta rawar da ya taka, amma yana neman a rage masa hukunci ya zama daidai da na sauran wadanda ake tuhuma.
