Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Zamfara, Dakta Jamil Jibo Magayaki, wanda ya sauya sheka tare da gwamna Dauda Lawal zuwa jam’iyyar APC, ya samu tikitin jam’iyyar domin tsayawa takarar kujerar mazabar Kaura Namoda ta Arewa a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara.
An bayyana hakan ne jiya ta bakin shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na APC a jihar Zamfara, Hon. Buba Galadima, yayin taron da aka gudanar a Karma Hotel da ke Gusau, inda Magayaki ya samu nasara ta hanyar amincewar wakilai.
Kwamitin ya ce wakilai 9,987 daga gundumomi biyar na mazabar ne suka tabbatar da Magayaki a matsayin ɗan takarar APC, abin da ke nuna irin goyon baya da amincewar da yake samu daga mambobin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki.
Bayan ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, Magayaki ya gode wa gwamna Dauda Lawal, shugabannin jam’iyya, wakilai da al’ummar Kaura Namoda ta Arewa bisa amincewar da suka nuna masa.
Ya kuma tabbatar wa magoya bayan jam’iyyar cewa zai yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar APC a babban zaɓe mai zuwa.
Haka kuma, ya yi kira ga dukkan mambobin jam’iyyar da sauran masu neman takara da su haɗa kai domin cigaban jam’iyyar da kuma bunƙasar mazabar Kaura Namoda ta Arewa da jihar Zamfara baki ɗaya.
