Kenneth Iwamasa, tsohon mataimaki na marigayi fitaccen jarumin Hollywood Matthew Perry, ya roki kotu da ta tausaya masa kafin yanke masa hukunci, yana mai cewa bai iya hana marigayin samun miyagun kwayoyi ba saboda yawan matsin lambar da yake fuskanta.
A wasu takardun kotu da aka gabatar kafin ranar yanke hukunci a ranar 27 ga Mayu, 2026, Iwamasa ya kalubalanci zargin masu gabatar da kara cewa zai iya kin bai wa tauraron shirin “Friends” sinadarin ketamine.
Iwamasa na fuskantar hukuncin zaman gidan yari bayan ya amsa laifin hada baki wajen rarraba ketamine. Ana zarginsa da taimakawa wajen samo miyagun kwayoyin tare da yi wa Perry allurar karshe a ranar 28 ga Oktoba, 2023, ranar da jarumin ya mutu sakamakon illar kwayar.
Lauyan Iwamasa ya bayyana a gaban kotu cewa wanda yake karewa ya aikata hakan ne bisa umarnin Perry a matsayinsa na ma’aikacin sa, ba wai da son ransa ba.
Lauyan ya ce masu gabatar da kara ba su fahimci irin matsin lambar da Iwamasa ke ciki yayin aiki tare da fitaccen jarumin ba.
Takardar kotun ta ce, “Ba zai iya kawai ya ce a’a ba. Rashin iya yin hakan ne ya haifar da mummunan sakamako,” inda aka amince cewa abin da ya aikata ya taimaka wajen mutuwar jarumin.
Wannan roko na neman sassauci ya biyo bayan wasikun tausayi da mahaifiyar Matthew Perry da ‘yar uwarsa suka aikewa kotu, inda suka dora laifi kan Iwamasa tare da zarginsa da cin amanar amincewar da Perry ya yi masa da kuma taimaka wa shan miyagun kwayoyin da suka kai ga mutuwarsa.
