Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Borno sun gano tare da lalata wani bam da aka ɓoye a cikin jakar baya a yankin Layin Logo, Moduganari a birnin Maiduguri.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Nahum Daso, ya ce an gano jakar ne da misalin ƙarfe 9 na safe a ranar Talata yayin da jami’an ke gudanar da sintiri da binciken tsaro a yankin.
Bayan gano jakar da ake zargin, jami’an sashen bama-bamai (EOD) na rundunar sun garzaya wurin, inda suka tabbatar da cewa akwai bam a cikinta, sannan suka lalata shi cikin aminci bisa ka’idojin aiki.
Rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga al’umma da su kasance cikin faɗa-a-ji da kuma kai rahoton duk wani abu ko mutum da ake zargi ga hukumomin tsaro.
Haka kuma ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike domin gano wanda ya ajiye jakar da kuma dalilin hakan.
