Shahararriyar mai tasiri a kafafen sada zumunta, Priscilla Ojo, ‘yar jarumar Nollywood, Iyabo Ojo, ta bayyana irin karamcin mahaifiyarta, tana mai cewa sau da dama gidan su na zama mafaka ga yara da dama.
Priscilla ta yi wannan bayani ne a wata hira da Chude Jideonwo, inda ta ce mahaifiyarta mace ce mai matuƙar tausayi da son taimakon jama’a.
Ta ce a wasu lokuta tana tashi daga barci ta tarar da yara daban-daban a gidan su, abin da ke sa ta ruɗewa tun tana ƙanana.
“Wani lokaci zan tashi na ga wani yaro a ɗakina, sai na tambayi mummy ‘Wacece wannan? Me yasa take kwance a gadona?’” in ji ta.
Ta bayyana cewa mahaifiyarta kan karɓi yara daga iyalai daban-daban ta ba su kulawa a gida.
Priscilla ta kuma yi wata magana mai ban mamaki inda ta ce mahaifiyarta ta taɓa shayar da ɗan’uwanta nono.
“Ta yi renon yara da yawa. Har ma ta taɓa shayar da ɗan’uwana nono. Hakan ya nuna irin zuciyar zinare da take da ita,” in ji ta.
Ta ce ta fito da wannan labari ne domin kare mahaifiyarta daga sukar da ake yi mata a kafafen sada zumunta, musamman lokacin da ake cece-kuce kan fina-finanta.
Priscilla ta kuma yaba da yadda mahaifiyarta ta rene su ita da ɗan’uwanta ita kaɗai bayan rabuwar aure, tana mai cewa ba ta taɓa jin rashin uba sosai ba saboda kulawarta.
“My mum ta taka rawar uwa da uba sosai a rayuwarmu,” in ji ta.
