Gwamnatin Jihar Kwara ta karyata rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ta kashe Naira biliyan 1.2 kan gadar Moro, wacce ke haɗa jihar Kwara da Jihar Oyo.
Ma’aikatar Ayyuka ta jihar ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakinta, Olajide Abolarin, ya sanya wa hannu.
Sanarwar ta ce zargin da wani mai suna “Ajibare Talks” ya yi a bidiyo na bogi ne kuma an shirya shi domin bata suna da kuma yaƙin neman siyasa.
A cewar ma’aikatar, gwamnatin jihar tana shiga tsakani ne duk lokacin da aka samu matsala da ta shafi rayuwar jama’a, ko da kuwa hanyar mallakar tarayya ce kamar gadar Moro Bailey.
Sai dai ta jaddada cewa dukkan ayyukan gyaran da aka yi a baya a gadar sun lakume Naira miliyan 27 ne kawai, ba Naira biliyan 1.2 ba kamar yadda aka yi ikirari.
“An yi amfani da N27m ne kawai wajen gyaran wucin gadi domin dawo da amfani da gadar, yayin da Gwamnatin Tarayya ke ci gaba da aikin sabuwar gada,” in ji sanarwar.
Ma’aikatar ta kara da cewa ba a taba kashe irin wannan makudan kudade ba a kowane mataki na wannan gwamnati dangane da gadar.
Ta kuma bayyana cewa ikirarin wani dan bidiyo cewa an kashe N1.2bn a lokacin jagorancin Hon. Abdulquawiy Olododo ƙarya ne da aka shirya domin bata masa suna da gwamnatin da ya yi aiki a cikinta.
Gwamnatin ta bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton, tana mai cewa dukkan ayyukan da aka yi a gadar sun kasance cikin sanin Gwamnatin Tarayya wacce ke da ikon kula da gadar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa bidiyon da aka wallafa an shirya shi ne domin kai farmaki na siyasa ga gwamnati da kuma wasu jami’ai.
