Shahararren mai kula da harkar nishadi a Najeriya, Ubi Franklin, ya yi bayani kan dalilin da ya sa wasu maza ke guje wa auren kotu, inda ya danganta hakan da ra’ayoyin da ba su da tushe game da rabon dukiya bayan saki.
A cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na X (Twitter na da), Franklin ya ce akwai fahimta mara inganci a tsakanin wasu maza cewa auren doka yana kaiwa ga rabon dukiya kashi 50-50 idan aka rabu.
Ya bayyana cewa wannan ra’ayi ba shi da tushe a dokar aure.
A cewarsa, biyan alimony (tallafin kuɗi bayan saki) ba ya takaita ga auren kotu kawai, domin kotu na iya ba da umarnin biyan tallafi ga kowanne bangare — namiji ko mace — idan sharuɗɗan doka sun cika, ko da a cikin auren gargajiya ne.
Franklin ya kuma yi magana kan batun dawo da kyaututtuka bayan karewar dangantaka, inda ya ce yawanci kyaututtukan da aka bayar ba sa dawowa sai idan an danganta su da wasu sharuɗɗa tun lokacin bayarwa.
Ya ba da shawara cewa mutane su rika sayen wasu kayayyaki da sunansu ko su fayyace sharuddan kyautar tun farko don kauce wa matsala daga baya.
Wannan bayanin nasa ya haifar da muhawara a kafafen sada zumunta, inda mutane ke tattaunawa kan gaskiyar dokokin aure da saki, tare da kalubalantar wasu tsoffin fahimta a tsakanin al’umma.
