Wani ɗan takarar gwamnan Jihar Yobe a ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Kashim Tumsah, ya karɓi fom ɗin takara gabanin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar.
Tumsah ya karɓi fom ɗin ne a hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar, inda ya bayyana aniyarsa ta shiga takarar gwamna a hukumance.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Tumsah ya yi alkawarin bin doka da oda tare da mutunta tsarin dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar.
Ya ce:
“Na shirya tsaf don shiga wannan tsari cikin gaskiya, adalci da kuma haɗin kan jam’iyya.”
Ya kuma yi kira ga magoya bayansa da su kasance cikin natsuwa, zaman lafiya da bin doka yayin tafiyar siyasa.
“Ina kira ga dukkan magoya bayana su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa, haɗin kai da jajircewa yayin da muke ci gaba,” in ji shi.
Tumsah, wanda ƙwararren lauyan harkar man fetur ne a matakin ƙasa da ƙasa, ya nuna damuwa kan rahotannin goyon bayan wani ɗan takara, inda ya ce hakan na iya kawo barazana ga haɗin kan jam’iyyar.
Ya ce:
“Goyon bayan ɗan takara ba tare da shawarwari da dukkan masu neman takara ba na iya lalata haɗin kai, adalci da daidaito a jam’iyyarmu.”
Ya kuma yi kira ga shugabancin APC na ƙasa da ke Abuja da su kasance tsaka-tsaki tare da tabbatar da sahihin zaɓen fidda gwani.
“Ina kira ga shugabanci na ƙasa da su kasance masu lura sosai tare da tabbatar da rashin nuna bangaranci. Duk wani ƙoƙari na karkatar da zaɓe ga wani na iya rage amincewar jama’a ga jam’iyyar,” in ji shi.
Tumsah ya kuma jaddada bukatar tabbatar da filin takara ɗaya ga dukkan ‘yan takara, yana mai cewa rashin adalci na iya rage martabar tsarin zaɓen jam’iyyar.
Ana sa ran APC za ta gudanar da zaɓen fidda gwani na gwamna a Jihar Yobe a cikin makonni masu zuwa.
