Hukuncin ya fito ne a ranar 21 ga Afrilu, 2026, daga Mai Shari’a D.H. Khobo na sashen shari’a na Kaduna, a shari’ar mai lamba KDH/KAD/ICPC/01/2026, wadda Hukumar Yaki da Cin Hanci (ICPC) ta shigar a madadin Gwamnatin Tarayya.
El-Rufai ya nemi belin ne ta hanyar takardar buƙata da ya gabatar a ranar 25 ga Maris, 2026, inda ya roƙi kotu ta ba shi beli “ko ta hanyar amincewa da kansa ko kuma duk wani sharadi da kotu za ta ga dama.”
Ya dogara da sashe na 35(4) da 36(5) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (da aka gyara), yana mai cewa laifukan da ake tuhumarsa da su ba na kisa ba ne, don haka ya cancanci beli.
Ya kuma bayyana cewa yana da alaƙa mai ƙarfi da al’umma, gidaje da kadarori, wanda a cewarsa ba zai ba shi damar tserewa ba.
El-Rufai ya kuma ce ya dawo Najeriya daga Masar a ranar 16 ga Fabrairu, 2026 domin amsa gayyatar EFCC, sannan ya soki ƙarar da ake masa da cewa tana da kurakurai kuma ba ta da ma’ana.
Haka kuma ya yi korafin rashin lafiya, yana mai cewa yana bukatar kulawar likitoci na musamman.
Sai dai ICPC ta yi adawa da bukatar nasa, inda ta ce tuhumar da ake masa mai nauyi ce kuma tana da alaƙa da zargin lalata tattalin arziki.
Hukumar ta kuma ce akwai yiwuwar El-Rufai zai iya tserewa ko kuma yin katsalandan a bincike da ake yi kan wasu da ake zargi.
ICPC ta kuma zarge shi da wani lamari a filin jirgin sama na Abuja a ranar 12 ga Fabrairu, 2026, inda ta ce ya hana jami’an tsaro gudanar da aikinsu.
A hukuncinsa, Mai Shari’a Khobo ya ce nauyin laifukan da ake tuhumar El-Rufai da su, tare da damuwar katsalandan a bincike, sun sa ba dacewa a ba shi beli a wannan mataki.
Ya ce: “Saboda girman tuhumar da ake yi masa da kuma damuwar cewa zai iya shiga binciken da ake yi, adalci ya fi dacewa a tabbatar da cewa zai kasance a hannun masu gabatar da ƙara har sai an fara shari’a.”
Kotun ta kuma ce El-Rufai ya gaza gabatar da isasshen hujjar likita kan rashin lafiyarsa.
Daga ƙarshe, kotu ta ce ya ci gaba da kasancewa a hannun ICPC har sai an fara shari’a, tare da umartar a gudanar da shari’ar cikin gaggawa a ranakun 1, 2, 3 da 4 ga Yuni, 2026.
