Babban Hafsan Tsaron Najeriya (Chief of Defence Staff), Olufemi Oluyede, ya umarci dakarun soji da su ƙara tsaurara farmaki kan ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, yana mai cewa dole ne a tabbatar da tsaron Najeriya “ko da wane hali ne.”
Ya yi wannan bayani ne a yayin ziyarar aiki ta farko ga dakarun da ke ƙarƙashin Operation Fansan Yamma a Gusau, Jihar Zamfara, inda ya ce ziyarar na da nufin duba shirin sojoji, magance ƙalubalen da suke fuskanta, tare da ƙara musu ƙwarin gwiwa a yaƙin da ake yi da ‘yan bindiga.
Ya ce:
“Umarnina ga dakarun soji a sarari yake: su fita su kawar da waɗannan masu laifi gaba ɗaya. Dole ne mu tabbatar da cewa Najeriya ta zama lafiya ko da wane hali ne,” in ji shi.
Oluyede ya jaddada ƙudirin rundunar soji na kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, yana mai cewa ci gaba da matsin lamba ga ƙungiyoyin masu aikata laifi zai taimaka wajen dawo da tsaro a yankin.
Dangane da buƙatar ƙarin tallafin jiragen sama domin taimaka wa sojojin ƙasa, CDS ya amince akwai ƙalubale, amma ya tabbatar da cewa gwamnati na ƙoƙarin ƙara inganta ƙarfin Nigerian Air Force.
Ya ce ana raba kayan aiki tsakanin fannoni daban-daban na aikin tsaro, amma gwamnati na aiki wajen samar da ƙarin kayan aiki domin tallafa wa dakarun ƙasa.
Haka kuma ya yabawa Gwamnatin Jihar Zamfara da al’umma bisa goyon bayan da suke bai wa ayyukan soji, yana mai cewa sabbin motocin yaƙi masu kariya daga harin bam (MRAP) sun taimaka wajen inganta aikin tsaro a yankin.
A ƙarshe, ya buƙaci haɗin kan al’umma musamman wajen bayar da sahihin bayanan sirri, yana mai cewa samun bayanai cikin lokaci na da matuƙar muhimmanci wajen karya lagon ‘yan bindiga.
