Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Arewacin Najeriya ta gargadi Kiristoci da su guji shiga muhawarorin addini masu cike da zagi da tashin hankali, tana mai cewa ba za a iya “kare Allah” ta hanyar zagi ko faɗa ba.
Shugaban CAN na Arewa, Joseph Hayab ne ya yi wannan gargadi a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Kaduna.
Hayab ya shawarci Kiristoci, musamman matasa da malamai, da su yi hakuri tare da kauce wa tayar da husuma yayin muhawarorin addini da ke ƙaruwa a kafafen sada zumunta.
Ya ce yawancin muhawarorin da ake yi a intanet da ake ganin kamar kare addini ne, a zahiri “muhawara ce marar amfani da mara fa’ida” wadda ke sa rikici da ƙara raba kan addinai.
A cewarsa, irin waɗannan muhawarori kan haifar da husuma da kuma abin da ya saɓa wa koyarwar addini.
Ya kafa hujja da ayoyin Littafi Mai Tsarki kamar Titus 3:9 da 2 Timoti 2:23, inda ya ce an umurci Kiristoci su guji rigingimu da ba su da amfani.
“Ni a matsayin shugaban addini, ba na koyarwa ko ƙarfafa kowane Kirista ya zagi addinin wani saboda an tsokane shi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa mai bin Kiristi ya kamata ya guji mayar da martani da tashin hankali, yana mai jaddada cewa “ba za a iya yin faɗa domin Allah ba,” amma a maimakon haka a rayu cikin zaman lafiya da fahimta.
