Ya bayyana haka ne a zantawarsa da kafar BBC, bayan da yan siyasa ke ci gaba da shiga jami’iyyar ta ADC.
Sheikh Khalil wanda ya taɓa yin takarar gwamnan Kano sau ɗaya, da kuma takarar neman zama ɗan takara gwamna a baya, ya kasance cikin waɗanda suka fi samun ƙuri’u a zaɓen 2023, a bayan jam’iyyun NNPP da APC da kuma PDP