Kwamitin Sa-ido kan Aiwatar da Manufofin Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC) ya bayyana Cibiyar Nazarin Kimiyyar Lafiya da Horarwa ta Biomedical Science Research and Training Centre (BioRTC) da ke Jami’ar Jihar Yobe a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun cibiyoyin binciken lafiya a Afirka.
Kwamitin ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin wata ziyara ta sa-ido da tantance ayyukan jami’ar, inda ya duba cibiyoyin bincike da sauran muhimman gine-ginen jami’ar.
Tawagar, wadda Kwamishinan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Jihar Borno, Dakta Maina Yaumi, ya jagoranta, ta zagaya ɗakin karatu na jami’ar, BioRTC, dakunan karatu, ɗakunan lacca da sauran muhimman wurare.
Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Muhammad Tahir, ya samu wakilcin Ma’ajiyar Littattafan Jami’ar, Dakta Amina Makintami, wadda ta jagoranci tawagar wajen zagayawa da jami’ar.
Da take tare da tawagar akwai Magatakardar Jami’ar, Alhaji Isa Audu Dallari; Bursar, Alhaji Mala Bulama Buni; Daraktan Ayyuka, Abubakar Dikko; Daraktan Tsare-tsaren Ilimi, Farfesa Ibrahim Umar; da Shugaban Ofishin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Mohammed Musa.
Da yake magana bayan kammala rangadin, Dakta Maina Yaumi ya ce kwamitin ya yi matuƙar mamakin irin ci gaban da jami’ar ta samu.
Ya ce, “Mun zagaya jami’ar kuma gaskiya abin ya ba mu mamaki. Mun ji daɗin abin da muka gani, domin ba mu yi tsammanin za mu ga irin wannan ci gaba ba.”
Ya bayyana cewa kwamitin zai rubuta rahoton abubuwan da ya gani, sannan ya tura dukkan matsalolin da aka gano ga hukumomin da suka dace domin neman mafita.
Sai dai ya ce Cibiyar BioRTC ta fi ba su mamaki, inda ya bayyana ta a matsayin wata cibiya ta musamman da za a iya kwatanta ta da manyan cibiyoyin binciken lafiya da ke nahiyar Afirka.
Ya ce, “BioRTC cibiya ce ta musamman. Tana daga cikin mafi kyawu ba kawai a Najeriya ba, har ma a Afirka. A wurare da dama da muka ziyarta, ba mu ga wata cibiya da za a iya kwatanta ta da ita ba.”
Ya bayyana cewa kwamitin zai ba da shawarar a gabatar da cibiyar ga Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa, domin ganin ta samu ƙarin shahara da karɓuwa a Najeriya da ƙasashen duniya.
Ya ce an buƙaci Daraktan BioRTC, Farfesa Mahmoud Bukar Maina, tare da mahukuntan jami’ar, su shirya cikakken bayani kan cibiyar domin Gwamnan Jihar Yobe ya gabatar da shi a gaban Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa.
A cewarsa, ɗaya daga cikin ayyukan kwamitin shi ne gano muhimman ayyuka irin wannan da ba su samu isasshen haske ba, yana mai cewa mutane da dama ba su san cewa irin wannan babbar cibiyar binciken lafiya tana cikin Jihar Yobe ba.
Ya ƙara da cewa ƙara tallata cibiyar da kuma ba ta damar samun ƙarin karramawa na iya jawo hankalin masu bincike, masu zuba jari, ƙungiyoyin bayar da tallafi da abokan hulɗa daga ƙasashen duniya zuwa Jami’ar Jihar Yobe.
Kwamitin ya ce irin wannan cibiya na da muhimmiyar rawa wajen bunƙasa binciken kimiyyar lafiya, horar da masana da kuma samar da sabbin dabaru da za su taimaka wajen inganta fannin lafiya a Najeriya da Afirka baki ɗaya
