Fargaba ta mamaye mazauna yankin Agbaje da ke kan hanyar Ala-Elefosan a ƙaramar hukumar Idanre ta Jihar Ondo, bayan da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace manoma uku.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka sace sun haɗa da mata biyu da namiji ɗaya, ciki har da wata mata mai suna Funke Falolu, yayin da suke aiki a gonarsu.
Wata majiya daga cikin iyalan waɗanda abin ya shafa ta ce masu garkuwar sun tuntubi iyalan tare da neman kuɗin fansa na Naira miliyan biyar ga kowane mutum kafin su sake su.
Majiyar ta bayyana cewa an kai rahoton lamarin ga Rundunar ‘Yan Sanda ta Ala da kuma jami’an tsaro na Amotekun domin ɗaukar matakin gaggawa.
Ta ce iyalan sun shiga cikin damuwa matuƙa, domin waɗanda aka sace sun tafi gona ne kamar yadda suka saba yi a kullum, amma ba su dawo gida ba.
Majiyar ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Ondo da hukumomin tsaro da su gaggauta ceto mutanen tare da ƙara tsaurara matakan tsaro, tana mai cewa manoma sun kasa zuwa gonakinsu saboda fargabar hare-haren masu garkuwa da mutane.
Da aka tuntuɓi Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ondo, Abayomi Jimoh, ya tabbatar da cewa rundunar za ta gudanar da bincike kan lamarin domin kamo masu hannu a satar tare da ceto waɗanda aka sace.
