Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya buƙaci Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ƙara ƙaimi wajen kare muhimman kayan aikin samar da wutar lantarki domin dakile yawaitar lalata su da masu laifi ke yi.
Tegbe ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Tunji Disu, a hedikwatar rundunar da ke Abuja.
Ministan ya ce lalata kayayyakin wutar lantarki na ci gaba da zama babbar barazana ga ɓangaren wutar lantarki, yana mai jaddada buƙatar ƙarin haɗin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Wutar Lantarki da Rundunar ‘Yan Sanda domin kare muhimman cibiyoyin samar da wuta.
Ya yabawa rundunar bisa ƙoƙarin da take yi wajen tabbatar da tsaro, tare da kira da a ƙara sa ido kan cibiyoyin wutar lantarki a faɗin ƙasar.
A nasa jawabin, Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Tunji Disu, ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da kare muhimman kayayyakin gwamnati tare da gurfanar da masu lalata kayan wutar lantarki a gaban kotu.
Ya kuma bayyana aniyarsa ta haɗa gwiwa da Ma’aikatar Wutar Lantarki wajen kafa wata runduna ta musamman domin kare kayayyakin wutar lantarki a faɗin Najeriya.
Ma’aikatar ta ce wannan haɗin gwiwa wani mataki ne na ƙarfafa tsaron kayayyakin wutar lantarki da tabbatar da ingantaccen samar da wuta ga al’ummar ƙasa, daidai da manufofin Renewed Hope Agenda na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
