Aƙalla mutum ɗaya ya rasu, yayin da fiye da mutane 30 ke ci gaba da ɓacewa bayan wani kwale-kwale ya kife a ƙauyen Malamawar Yan Dutse da ke Ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa.
Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne da yammacin Lahadi yayin da kwale-kwalen ke ɗauke da manoma da ma’aikatan gona, ciki har da mata, suna dawowa daga gonakinsu zuwa ƙauyensu.
Majiyoyi daga yankin sun ce akwai fiye da fasinjoji 40 a cikin kwale-kwalen lokacin da hatsarin ya faru.
Hukumar SEMA ta Jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta tare da masu iyo na yankin da sauran hukumomin ceto na ci gaba da aikin ceto domin gano waɗanda suka tsira da kuma waɗanda har yanzu ake nema.
Shugaban Kwamitin Ba da Agajin Gaggawa na Ƙaramar Hukumar Ringim, Malam Habibu Dauda, ya buƙaci al’umma su kwantar da hankalinsu, su kuma guji yaɗa rahotannin da ba a tabbatar da su ba har sai hukumomi sun fitar da cikakken bayani.
