Tsohon jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) kuma masanin harkokin siyasa, Farfesa Babafemi Badejo, ya ce bayan nasarar ceto ɗalibai da malamai da aka sace a Oriire na Jihar Oyo, lokaci ya yi da za a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma ɗaukar darasi.
Badejo ya yabawa jami’an tsaro bisa nasarar ceto mutanen bayan kwanaki 56 a hannun masu garkuwa da mutane. Haka kuma ya jinjinawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Seyi Makinde kan rawar da suka taka wajen ganin an ceto waɗanda aka sace.
Sai dai ya ce bai kamata a tsaya da murnar ceto ba, domin akwai buƙatar bincike mai zurfi kan yadda lamarin ya faru da kuma yadda za a hana sake aukuwarsa a gaba.
Ya kuma soki kiran da Gwamna Makinde ya yi na neman Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta gudanar da bincike kan lamarin, yana mai cewa UN ba ta da ikon gudanar da irin wannan bincike a cikin ƙasa sai idan gwamnatin tarayya ta nema ko kuma Kwamitin Tsaron Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayar da izini.
A cewarsa, Najeriya na da hukumomi da ƙwararrun jami’an da za su iya gudanar da bincike tare da hukunta masu hannu a laifin ba tare da sa hannun ƙasashen waje ba.
Badejo ya bukaci gwamnati da ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai su ci gaba da matsa lamba domin a bayyana gaskiyar abin da ya faru, tare da ɗaukar matakan da za su hana irin wannan iftila’i sake faruwa nan gaba.
