Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya gudanar da garambawul a majalisar zartarwar jihar, inda ya sallami wasu kwamishinoni tare da amincewa da murabus na wani kwamishina.
A cikin sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamna, Mukhtar Gidado, ya fitar, an bayyana cewa Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari, Mohammed Salis Gamawa, da tsohon Kwamishinan Ilimi wanda daga baya aka mayar zuwa Ma’aikatar Wutar Lantarki, Kimiyya da Fasaha, Dr. Lawal Rimin Zayam, sun fita daga majalisar zartarwa nan take.
Haka kuma gwamnan ya amince da murabus ɗin tsohon Kwamishinan Raya Karkara da Ayyuka na Musamman, Faruk Mustapha.
Sanarwar ta ce gwamnan ya tura sunayen waɗanda ake son su maye gurbin waɗanda suka fita, tare da sauran waɗanda za su cike guraben da ke cikin majalisar zartarwar, zuwa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi domin tantancewa da amincewa.
Gwamna Bala Mohammed ya gode wa kwamishinonin da suka sauka bisa gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar, tare da yi musu fatan alheri a rayuwarsu ta gaba.
Ya kuma jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da gina gwamnati mai inganci, gaskiya da kuma hidima ga al’ummar Jihar Bauchi.
